10 Satumba 2020 - 09:49
​Sudan: Ambaliyar Ruwa Ta Rushe Dubban Gidajen Jama’a

Dubun-dubatar mutane ne suke bukatar agajin gaggawa a kasar Sudan, bayan da ambaliyar ruwa ta rushe gidajensu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, sakamakon tafka ruwan sama da ake ta yi kamar dab akin kwarya akasar Sudan, dubban gidajen jama’a ne suka rushe, yayin mutane fiye da 100 suka rasa rayukansu.

Rahoton y ace yanzu haka akwai dubban mutane wadanda suke bukatar agajin aggagwa bayan da suka rasa komai nasu a cikin gidajensu da suka rushe.

Jama’a da dama da lamarin ya shafa suna kokawa kan rashin tabuka komai daga bagaren gwamnatin kasar wajen taimaka musu bayan faruwar lamarin.

Sai dai a nata bagaren hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, tuni ta fara kai agajin gaggawa ga mutanen da ambaliar ruwan ta raba da muhallansu a kasar ta Sudan, inda ta raba musu wasu daga cikin kayayakin da suke bukata da gaggauwa, da suka hada da abinci mai saukin sarrarafawa, da kuma barguna da katifu.

342/